A wasu hotuna da rundunar sojin Najeriya ta fitar, an nuna yadda dakarunta suka samu nasarar kashe ƴan ta’adda da dama tare da rusa sansanonin su a yankin tsaunin Mandara, da ke cikin jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ƴan ta’addan dai na Boko Haram sun jima suna haddasa tarzoma a yankin, inda suke kashe fararen hula, garkuwa da mutane, da kuma kai farmaki a wasu sassan jihohin Arewa maso Gabas.
Bayan wani sabon farmaki da suka kaddamar a ‘yan kwanakin baya, wanda ya shafi rayuwar jama’a kai tsaye, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta kara tsaurara matakan tsaro da kawo dauki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Harin bam da sojoji suka kai kan sansanin ‘yan ta’adda a tsaunin Mandara na iya zama wata gagarumar nasara wajen dakile barazanar da Boko Haram ke ci gaba da yi wa zaman lafiyar kasar gaba ɗaya.
KU BIYO MU A FACEBOOK