">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Saturday, August 16, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Haryanzu Ba’a Ga Mutane Sama da 700 Ba Tun Bayan  Ambaliya a Mokwa – Gwamnatin Neja 

by Abubakar Ismail kankara
June 18, 2025
in Labarai
0
mummunar ambaliya
Share on FacebookShare on Twitter
">

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa fiye da mutane 700 har yanzu ba a gansu ba bayan mummunar ambaliya da ta afku a karamar hukumar Mokwa na jihar.

Gwamna Umaru Bago ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi bakuncin Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon jami’in tsaron marigayi Janar Sani Abacha, da wasu abokansa da suka kai ziyarar jaje bisa ibtila’in ambaliyar da ta auku a Minna a ranar Talata.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta, ya ce mutane 207 sun mutu, kana gidaje fiye da 3,000 sun lalace sakamakon iftila’in.

“Fiye da mutane 700 sun bace kuma har yanzu ba mu san inda suke ba. Ambaliyar ta haifar da barna mai yawa,” in ji Gwamna Bago.

Ya ƙara da cewa, gidaje 400 sun samu lahani, inda 283 daga ciki suka rushe gaba ɗaya, har da shaguna 50 da aka lalata.

RelatedPosts

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

Kasa da Awa Ɗaya Bayan Ya Wallafa Cewa Tsaro Ya Inganta, ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shi

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Tsohon Kwamishina a Katsina

Ana Neman Tallafin Jama’a Domin Ceto Jariri da Aka Haifa da Cutar Gastroschisis a Jigawa

Gwamnan ya gode wa mutane da hukumomi da suka kawo gudunmawa da agaji, yana mai cewa wannan bala’i ya shafi kasa baki ɗaya, ba jihar Neja kawai ba.

Ya ce gwamnati na aiki da masana don gano musabbabin ambaliyar, kuma ana jiran sakamakon binciken.

A nasa jawabin, Hamza Al-Mustapha ya ce sun zo ne domin yi wa gwamnatin Neja da mutanen Mokwa ta’aziyya bisa iftila’in da ya faru.

“Mun zo ne don nuna alhini bisa asarar rayuka da dukiyoyi. Muna fatan hakan ba zai kara faruwa ba,” in ji shi.

Ya ce tawagar ta kunshi manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar, kuma sun zo ne da niyyar ba da tallafi da shawarwari ga gwamnati da al’umma.

Ya bayyana cewa za su gana da majalisar gargajiya ta Mokwa, don tattaunawa kan hanyoyin da za a magance irin wannan iftila’i a nan gaba tare da inganta tsare-tsaren birane da yanayin zama.

">

Bayan haka, Al-Mustapha da tawagarsa sun kai ziyara ta girmamawa ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd.).

">

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

by Abubakar Ismail kankara
August 16, 2025
0

A dai-dai lokacin da ake fama da yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a fadin arewacin kasar nan, mai...

Tsaro Ya Inganta

Kasa da Awa Ɗaya Bayan Ya Wallafa Cewa Tsaro Ya Inganta, ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shi

by Abubakar Ismail kankara
August 15, 2025
0

Rahotan da Daily Episode Hausa ta tattara daka jaridar idon mikiya na nuna da cewa, yan bindiga dake yawan kashe...

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Tsohon Kwamishina a Katsina

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Tsohon Kwamishina a Katsina

by Humaira Muhammad
July 30, 2025
0

Babbar Kotun Jihar Katsina mai lamba 9, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu...

cutar gastroschisis

Ana Neman Tallafin Jama’a Domin Ceto Jariri da Aka Haifa da Cutar Gastroschisis a Jigawa

by Abubakar Ismail kankara
July 30, 2025
0

Kasa da sa’o’i 24 da haihuwarsa, jariri mai suna Salisu Sale wanda aka haifa da cutar gastroschisis – wata larura...

ambaliya

An buƙaci ‘yan Kano da Jigawa da ke kewayen Tiga Dam da su tashi saboda fargabar ambaliyar ruwa

by Abubakar Ismail kankara
July 25, 2025
0

Biyo bayan hasashen da Hukumar Yanayi ta Ƙasa (NiMet) da Hukumar Kula da Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) suka fitar, wanda...

Jamil Mabai

Gwamnan Katsina ya naɗa Jamil Mabai a matsayin Mataimaki na Musamman

by Abubakar Ismail kankara
July 19, 2025
0

A wani mataki na ƙarfafa shugabanci da inganta hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar...

Next Post
MAGANIN BARAYIN WAYA

MAGANIN BARAYIN WAYA

Rokon Ruwan Sama

An Gudanar da Sallar Rokon Ruwan Sama a Kaura Namoda - Jihar Zamafara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In