Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya bada umarnin rufe duk makarantun kwana dake jahar biyo bayan harin da yan bindiga suka kai kwalejin mata dake Jangebe.
Yan bindigan sun kai farmaki makarantar ne a cikin daren Juma’a, 26 ga watan Feburairu, inda suka yi awon gaba da fiye da dalibai mata 300.
Home Hausa News Harin Jangebe: Matawalle ya rufe duk makarantun kwana a jahar Zamfara
Hausa News
Harin Jangebe: Matawalle ya rufe duk makarantun kwana a jahar Zamfara
by
SHARP REPORTERS
43 mins ago
0
-ADVERTISEMENT-
Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya bada umarnin rufe duk makarantun kwana dake jahar biyo bayan harin da yan bindiga suka kai kwalejin mata dake Jangebe.
Yan bindigan sun kai farmaki makarantar ne a cikin daren Juma’a, 26 ga watan Feburairu, inda suka yi awon gaba da fiye da dalibai mata 300.
Harin Jangebe: Fusatattun Iyayen yara sun yi rikici da hukumar makaranta, sun tafka barna
Jangebe: Ba mu san adadin dalibai mata da yan bindiga suka sace ba – Gwamnatin Zamfara
Sharpreporters.com ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar jahar inda ya bayyana damuwarsa game da abin takaicin daya faru a Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara.
Gwamnan ya jajanta ma al’ummar jahar, musamman iyaye da yan uwan daliban da aka yi garkuwa dasu. Sa’annan ya bada tabbacin gwamnati na yin duk mai yiwuwa don ceto daliban daga hannun miyagun.
“A yanzu haka jiragen Yansanda da sauran jami’an tsaro na cigaba da bin sawun yan bindigan, kuma zamu cigaba da sanar da iyayen daliban halin da ake ciki a kowanne mataki.
“A matsayina na uba ina jin zafin duk iyayen da aka dauke musu yara. Ina kira ga iyaye su yi hakuri, su cigaba da addu’a don samun nasarar aikin da muka sanya a gaba na ceto daliban nan.
“Duk da wannan tasgaro da aka samu, gwamnatina za ta cigaba da tsarin sulhu da karbe makami daga hannun tubabbun yan bindiga, saboda kasancewar harsashi daya a hannun miyagun mutum ka iya sanadiyyar cutar da mutumin kirki da bai ji ba, bai gani ba.” Inji shi.
Gwamnan ya kara da cewa: “Yayin da muke kokarin karfafa tsaro a makarantunmu, na bada umarnin kulle dukkanin makarantun kwana dake fadin jahar nan gaba daya.
“Haka zalika ina mika kokon bara ga gwamnatin tarayya don magance matsalar tsaro da muke fuskanta a jahar. Da fatan Allah Ya bamu nasara a wannan muhimmin aiki da muka sa a gaba. Amin.” Inji shi.