Matafiya akan hanyar Katsina zuwa Jibia na cigaba da kokawa akan rashin kyawon hanya musamman a wuraren, Mil Takwas, Farun Bala, Ƴan Farurruka, Ƴan Nono, Kukar Babangida, Makera da Kwarare.
Dayawa matafiyan sukan koka ne cewa banda matsalar barazanar rashin tsaro da hanyar take fama dashi wanda kusan babu ranar da ɓarayin daji basu yunƙurin kai farmaki a hanyar, hanyar tana buƙatar kulawa musamman a wuraren da muka ambata a sama domin ɓarayin dajin sukan yi amfani da rashin kyawon hanya wajen yunƙurin ɗaukar matafiyan.
Ko a jiya Laraba 08/01/2025 an samu hatsari akan wannan hanyar Katsina zuwa Jibia saboda rashin kyawon hanyar inda har aka rasa ran Mutum guda.
Da wannan Al’umma suke jan hankalin Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dr. Dikko Umaru Radda da ta duba yiyuwar gyara masu wannan hanyar saboda Muhimmancin da hanyar take dashi ga ƴan ƙasa dama Baƙi dake shigowa ƙasar domin huddatayyar kasuwanci a kowace rana.