Gwamnatin Saudiyya ta amince a gudanar da jana’iza tare da binne marigayi kuma attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a birnin Madina – daya daga cikin biranen masu tsarki a ƙasar Saudiyya.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar marigayin da ta auku a safiyar Asabar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya kwanta dama bayan doguwar jinya.
A cewar Babban Sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye da suka dace, kuma hukumomin Saudiyya sun amince da bukatar iyalan marigayin na a binne shi a garin Madina.
“Alhamdulillah an samu amincewar hukumomi. Za a ɗauki marigayin daga Abu Dhabi zuwa Madina domin gudanar da jana’iza da binnewa gobe da safe, in sha Allah,” in ji Mustapha.
Iyalansa sun bayyana cewa burin marigayin tun a rayuwarsa shi ne a binne shi a birnin Madina – birnin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya rayu kuma aka binne shi.
Ko da yake an dakatar da binnewar nan take, an gudanar da sallar jana’iza ga marigayin a Kano a matsayin sallar ga’iba, wadda fitaccen malamin addini, Sheikh Ibrahim Khalil, ya jagoranta tare da dimbin jama’a da suka halarta.
Marigayi Alhaji Aminu Dantata, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan kasuwa da masu taimakon al’umma a Najeriya, ya bar tarihin gado mai ɗimbin daraja a bangaren kasuwanci da jin ƙai ga marasa ƙarfi.
KU BIYO MU A FACEBOOK