Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Alhaji Abubakar Hassan, mamallakin Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, ya ce har yanzu gwamnati bata tuntubi hukumar makarantar ba saboda sace daliban da aka yi.
A wani sakon murya da aka turawa manema labarai a ranar Laraba, Alhassan yace masu garkuwa da mutanen sun tuntubesu inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan dari.
“Har yanzu gwamnati bata shiga cikin lamarin ba. Sakataren gwamnatin jihar ya tuntubemu ta bakin matarsa saboda muna da alaka da ita. Ta kira ni kuma ta mika wayar ga mijinta wanda yace suna addu’ar dawowar yaran kuma har a yanzu bai zo mana jaje ba,” yace.
Ya kara da cewa yayi kokarin samun shugaban karamar hukumar amma ya sanar da cewa yana wasu ‘yan kokari ne.
A daya bangaren, gwamnatin jihar tace tana dukkan kokarin da ya dace wajen ganin an sako yaran makarantar cikin koshin lafiya.