Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Magantu Kan Sace Ɗalibai Mata 300 Inda Ta Bayyana Matakin Da Ta Ɗauka
Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dauran ya tabbatar da satar ɗalibai mata 300 a jihar.
Da yake magana da manema labarai yace yanzu haka yana kan hanyar zuwa Jangebe dake Talatar Mafara inda aka sace ɗaliban.
Yace sun kuma aika jami’an tsaro dan bin sahun wanɗanda suka sace ɗaliban, ya kuma bayana cewa ba zai iya faɗar yawan ɗaliban da aka sace ba sai ya je makarantar tukuna.
Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa an sace dalibai da suka kai 300.