Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta haramta shan taba sigari a bainar jama’a don magance annobar shan tabar, yayin da Najeriya ta yi ƙiyasin cewa mutum 16, 100 ne ke mutuwa duk shekara dalilin cutukan da suka danganci shan tabar.
Jaridar ta ruwaito cewa wannan yunƙurin zai taimaka wurin inganta lafiyar al’ummar jihar .
Daily Tryst ta ruwaito Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa kwamishinan lafiya na jihar yana cewa gwamnatin na aiki ba dare ba rana wurin ganin ta rage yawan mutane masu shan taba a jihar.
Ya kuma ce akwai wani ƙudirin doka a halin yanzu a majalisar dokokin jihar da ake fatan za ta samar da hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi wadda za a ɗora wa alhakin tabbatar da cewa shan miyagun ƙwayoyi ya ragu a jihar.