Gwamnatin jihar Ekiti ta bai wa manoma da makiyaya wa’adin makwanni biyu, su yi rijista da gwamnatin jihar ko kuma su fice daga jihar baki daya.
Tuni wa’adin ya fara aiki tun ranar Lahadi, 22 ga watan Maris.
Cikin wata sanarwar kwamishinan aikin gona da wadatar abinci na jihar Dakta Olabode Adetoyi, ya bayyana cewa gwamnati ta lura cewa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya na haifar da haɗari ga lafiyar mutane da kuma ƙoƙarin wadata jihar da abinci, don haka ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi ga gwamnati, don dakile matsalar.
A watan Fabrairun da ya wuce ne jihar ta gudanar da rajista ta tsawon makwanni biyu, ga manoma da makiyaya, sai dai hukumomi sun ce ba dukkaninsu ne suka yi ba.
Mashawarci na musamman ga Gwamna Kayode Fayemi kan lamuran tsaro kuma shugaban kwamitin sasanta makiyaya da manoma a jihar Birgediya-Janar Ebenezer Ogundana mai ritaya., ya yi gargadi a cikin sanarwar, yana cewa ”Za a kori duk wanda ya ƙi yin wannan rajista daga jihar’