Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na rage farashin kayayyakin abinci ta hanyar zuba jari mai yawa a harkar noma.
Mohammed Idris ya bayyana haka ne a Abuja ranar Talata a wani taron manema labarai don fara taron tattaunawa da ministoci na shekarar 2025.
Ya jaddada cewa, duk da cewa gwamnati ba za ta sanya takunkumin hana sayar da kayayyakin abinci ba, bisa ka’idojin tattalin arziki, gwamanti za ta ci gaba da mayar da hankali wajen rage farashin ta hanyar bunkasa noma.
Ministan ya bayyana shekarar 2025 a matsayin shekara ta hadin gwiwa, bisa irin ci gaban da aka samu a watanni 19 na gwamnatin Tinubu a daidai lokacin da ta ke gab da cin rabin wa’adin mulkinta.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X