Bayan kafa tsarin bashi ga ɗaliban Najeriya, wanda nufinsa shi ne bai wa matasa damar samun ilimi cikin sauƙi da kuma hana barin makaranta, gwamnatin tarayya ta ƙara ɗaukar mataki ta hanyar ƙaddamar da sabon shirin TVET domin koyar da matasa da ɗalibai dabarun sana’a da basira don su sami nasara a rayuwa.
A wajen wani taron wayar da kan al’umma da aka gudanar a Kaduna, wanda kamfanin G-Adams Integrated Service Limited ya shirya ƙarƙashin taken: “Matasa ta Hanyar Kwarewa: Sabuwar Fuskar TVET a Najeriya”, Daraktan Ayyuka na Shirin, Mustafa Iyal, ya bayyana yadda shirin ke da burin magance matsalar rashin aikin yi a ƙasar.
A cewarsa: “A Najeriya, mun saba da shirye-shiryen kasuwanci da koyon sana’a, amma idan aka duba tsarin da dabarun da aka gina wannan shiri da su, zan iya tabbatar muku cewa wannan na daga cikin mafi inganci da ƙasar nan ta taɓa samu, duba da irin tasirin da zai haifar a cikin ƴan shekaru masu zuwa.”
“TVET yana da rassa guda uku: Na farko, akwai ‘master twelve’ wanda yana ɗaukar shekara guda inda kowane mai nema zai sami horo na cikakken shekara. Sai kuma ‘master six’ wanda zai ɗauki tsawon shekaru shida. A ƙarshe kuma, akwai shirin federal technical colleges tracking, wanda manufarsa ita ce taimaka wa makarantun fasaha da ɗalibansu don ƙara inganci da samar da ayyukan yi,” in ji Iyal.
Ya ƙara da cewa horon kyauta ne gaba ɗaya, kuma an haɗa ƙwararrun ƙungiyoyi da dama a cikin shirin, yana kuma roƙon jama’a su amfana da wannan dama.
“An tanadar da horo kyauta gaba ɗaya. Gwamnati za ta biya kuɗin horon, sannan kuma za ta rika biyan kowane mahalarta ₦20,000 a kowane wata a matsayin alawus. Bayan kammala horon, za a ba su kayan aiki da na’ura a matsayin jari don fara sana’arsu,” in ji shi.
“Wannan dama ce ga kowane ɗan Najeriya, ko daga Arewa ko Kudu, matuƙar kana da ƙasar nan, kana da damar neman shiga shirin TVET.”
Ya ƙara da cewa abubuwan da ake buƙata domin shiga shirin ba su da yawa. “Kawai katin shaida na ƙasa (NIMC), lambar waya, da kuma BVN kawai ake buƙata,” in ji shi.
A ƙarshe, Mr. Iyal ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi shirin TVET domin ci gaban ƙasa.
KU BIYO MU A FACEBOOK