Gwamnatin Tarayya ta samar da wani tsari don tabbatar da gaskiya, inganci, da kariya ga masu bada sassan jikinsu don dashen ga marasa lafiya.
A wajen bikin kaddamar da ƙa’idojin aikin dashen a Najeriya, ƙaramin ministan lafiya da walwalar jama’a, Dr. Isyak Adekunle Salako, ya bayyana cewa sabbin ka’idojin za su tabbatar da amincin bada gudunmawar sassan jiki bisa karɓaɓɓan tsarin dashen duniya.
Gwamnati za ta tantance asibitocin da ke gudanar da dashen da cire sassan jiki don tabbatar da bin ƙa’idoji. Ministan ya ce amincewa da ƙa’idojin ranar 13 ga watan Nuwamba, 2024, wata gagarumar nasara ce a kokarin tabbatar da inganci da kariya a fannin dashen sassan jiki a Najeriya.
KU BIYO MU A FACEBOOK