A wani mataki na ƙarfafa shugabanci da inganta hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya naɗa Jamil Mabai a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa da kafafen yaɗa labarai na zamani.
Sanarwar naɗin, wanda aka fitar a wasika mai ɗauke da kwanan wata 16 ga Yuli kuma aka sanya wa hannu daga sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari, ta bayyana cewa an zaɓi Mabai ne bisa sahihin imani da jajircewarsa wajen aiki da kishin ƙasa.
Jamil Mabai dai ya shahara a matsayin ƙwararren masani a fannin sadarwa, da kuma bincike, inda ya kwashe sama da shekaru goma yana gudanar da aikinsa a wannan fanni. Kafin wannan naɗi, ya kasance wakilin News Central a Katsina, inda ya fito da rahotanni masu ƙayatarwa kan yadda matsalolin tsaro ke ta’azzara a jihar da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.
Yazuwa yanzu, ana tsammanin sabon naɗin zai taimaka wajen sake fasalin yadda gwamnatin jihar ke wallafa bayanai ta kafofin sadarwa zuwaga ga jama’a, tare da bayyana musu a sarari abubuwan da gwamnati ke aiwatarwa da yadda suke shafan rayuwarsu ta yau da kullum.
KU BIYO MU A FACEBOOK