">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Monday, October 13, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Gwamnan CBN Da Hafsan Sojan Kasa Sun Ki Amsa Gayyatar Majalisa

by Abubakar Ismail kankara
March 23, 2021
in Sport Stories
0
Gwamnan CBN Da Hafsan Sojan Kasa Sun Ki Amsa Gayyatar Majalisa
Share on FacebookShare on Twitter
">

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Attahiru Ibrahim da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun yi watsi da goron gayyatar Majalisar Wakilai wacce ta nemi su bayyana a gabanta domin fayyace wasu batutuwa da suka danganci kudin siyan makaman sojoji.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa basu amsa goron gayyatar Majalisar ba wacce ta nemi su bayyana gabanta a ranar 12 ga watan Maris

Majalisar ta kafa wani kwamitin wucin gadi ne don bincikar harkallar siyo makaman sojoji da kuma na sauran hukomomin tsaro a kasar, ta aike da sammacin ga Gwamnan Babban Bankin da kuma Babban Hafsan Soji amma suka yi mata kunnen uwar shegu.

Gayyatar na zuwa ne bayan wani dan majalisar daga Jihar Imo, Bede Eke ya gabatar da bukatar hakan yayin zaman majalisar na ranar Litinin ta makon da ya gabata.

RelatedPosts

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

Kano Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Cutar Murar Tsuntsaye

Yayin gabatar da kudirin, Honarabul Eke ya ce sammacin ya zama tilas ne biyo bayan kin amsa goron gayyatar da manyan jami’an gwamnatin biyu suka yi.

A cewarsa, ya kamata Majalisar ta fara daukar matakai masu tsauri a kan jami’an gwamnati masu kin amsa goron gayyatar da ta yi musu a duk lokacin da ta bukata.

“Majalisar tana fuskantar matsaloli da Babban Bankin Najeriya kuma ba zai yi wa mu ci gaba da zuba masa idanu ba don da bazarmu yake taka rawa kasancewar sai mun amince da kasafin kudinsa kafin ya gudanar da ayyukansa yadda ya dace.”

“Abun da kawai muke bukata shi ne Babban Bankin ya yi mana bayani dalla-dalla a kan yadda yake fitar da kudin sayo makamai.”

">

“Idan kuma akwai abun da suke boyewa, ba za mu kyale ba domin a kullum ana kashe mutane saboda haka ba zai yiwu mu rika bata lokaci muna zaman jiran wata hukuma ta gwamnati ba.”

“Ina kira da a aike wa Babban Hafsan Sojin Kasa da kuma Gwamnan Babban Bankin sammaci, don haka ne kadai zai sanya su fahimci mun dauki lamarin da muhimmanci,” inji shi.

Honarabul Eke ya ce sau hudu Majalisar tana gayyatar Babban Hafsan Sojin kasa yayin da ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin sau biyar amma babu karo daya da suka amsa goron gayyatar.

DAILY RPISODE HAUSA

">

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

 

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Gobarar Tankar Fetur

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Mutane da dama, ciki har da wata mai juna biyu, sun rasu yayin da gobara ta tashi lokacin da suke...

harin jiragen Sojin

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Iyalan waɗanda harin jiragen Sojin saman Najeriya ya rutsa da su a Zamfara sun nemi gwamnati ta biya su diyya...

Asusun Bai Ɗaya

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa, daga ƙarshen watan Janairu, dukkan kananan hukumomi a Najeriya za su fara karɓar...

Murar Tsuntsaye

Kano Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Cutar Murar Tsuntsaye

by Abubakar Ismail kankara
January 17, 2025
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk...

Biden da Netanyahu sun tattauna kan tsagaita wuta a Gaza

Biden da Netanyahu sun tattauna kan tsagaita wuta a Gaza

by Abubakar Ismail kankara
January 13, 2025
0

Shugaban Amurka, Joe Biden da Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun tattauna ta waya a daidai lokacin da ake ci gaba...

rikicin masarautar Kano

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Umarci Sake Sauraron Shari’ar Rikicin Masarautar Kano

by Abubakar Ismail kankara
January 10, 2025
0

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin sake sauraron shari’ar rikicin masarautar Kano da ya haɗa da...

Next Post
Wata mata ta lakadawa Kishiyarta duka har lahira, Takuma Kona Gawar A Garin Minna

Wata mata ta lakadawa Kishiyarta duka har lahira, Takuma Kona Gawar A Garin Minna

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In