Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsayarsa na ƙin amincewa da sulhu da ’yan bindiga na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin karɓar bakuncin Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar, wanda ya ziyarci jihar domin yin ta’aziyya kan harin bam da rundunar sojin sama ta kai bisa kuskure.
Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sauya matsayarta ba game da ƙin sasanci da miyagun mutane. A nasa bangaren, Air Marshal Abubakar ya gode wa gwamnan bisa fahimtarsa cewa harin da aka kai ba da gangan ba ne.