Gwamna Aminu Bello Masari ya jajantawa dangin Marigayi Grand Kadi Usman Muhammad da ke Daura, kan rasuwar daya daga cikin ‘yayanta Kadi Sa’eed Usman Muhammad.
Da isar Kofar Arewa, babban yayan marigayin ya tarbi Gwamnan wanda kuma shi ne Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Ahmed Usman El Marzuk da wasu ‘yan uwa.
Gwamnan tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar Malam Shitu S. Shitu, da Kwamishinan Kasuwanci Alhaji Mukhtar Gidado Abdulkadir da wasu hadimansa na musamman sun yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa mamacin ya kuma baiwa Iyalin karfin jure rashin.
Da yake amsawa a madadin dangin, Barista Ahmed Usman El Marzuk ya gode wa Gwamnan bisa wannan ta’aziyya da addu’ar.
Khadi Sa’eed Usman Muhammad wanda har zuwa rasuwarsa Kadi (Alkali) na Kotun daukaka kara ta Shari’a ta jihar, ta mutu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Katsina a ranar Talatar da ta gabata bayan gajeruwar rashin lafiya.
Kadi dan shekara hamsin da uku ya bar mata hudu, ‘ya’ya goma sha uku da dangi da dama.
Allah yasa ransa ya huta, Ameen.