">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Wednesday, October 15, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Haddasa Rashin Tsaro Da Kabilanci A Nijeriya – Jigon Jam’iyyar APC

by Abubakar Ismail kankara
April 12, 2021
in Music
0
Share on FacebookShare on Twitter
">

Wani jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa, ba za a taba samun daidaituwa a Nijeriya har sai ‘yan siyasa sun rika amfani da fadin gaskiya wajen cin zabe a kasar nan.

Haka kuma jigon jam’iyyar APC mai suna Saliu Mustapha dora alhakkin rashin tsaron da ke faruwa a kasar nan a kan karairayin da ‘yan siyasa ke shirgawa a lokacin da suke kokarin cin zabe. Mustapha wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na reshi, ya bayyana haka ne a wurin gabatar da wani littafi wanda wani tsohon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kwara, Iyiola Oyedepo ya rubata. Littafin mai suna, ‘karairayi 21 da ‘yan siyasa ke shirga wa talakawa don su zabe’, an kaddamar da shi ne a Ilorin babban birnin Jihar Kwara. Baya ga shugabancin APC a Jihar Kwara, marubucin ya kuma taba zama kwamishina duk dai a Jihar Kwara dai.

A wurin gabatar da littafin dai, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazak da Ministan yada labarai, Lai Mohammed duk sun tura wakilai.

Babban mai kaddamarwa Mustapha, ya kuma kara da cewa, “idan za mu fada wa kan mu gaskiya a matsayinmu na jiga-jigan ‘yan siyasa, to kowa ya san cewa kokarin cin zaben da muke yi da tsiya ko da arziki, ko a ci ko a mutu, duk su ne suka haifar da matsalar tsaro da tayar da jijiyoyin kabilanci da bangaranci da ke addabar kasar nan a halin yanzu.”

RelatedPosts

Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

APC ba Ta isa Ta kwashe shekara 36 Tana Mulki ba – PDP

An ji cewa, tsohon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kwara, Iyiola Oyedepo, ya bayyana cewa, littafinsa mai suna “karairayi 21 da ‘yan siyasa ke shirga wa talakawa lokacin yakin neman”, ya rubuta sune domin fallasa dabarun da ‘yan siyasa ke yi idan su na neman kuri’u daga hannun jama’a. Oyedepo ya yi wannan furucin a Ilorin babban birnin Jihar Kwara, a lokacin da yake gabatar da littafin ga jama’a.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, littafinn mai shafuka 140, ya kunshi babi 21 na karairayi 21 da ‘yan siyasa ke yi domin ribbatar talakawa su jefa masu kuri’a. Marubucin littafin ya bayyana cewam, ya rubuta littafin ne domin ya ilmantar da talakawa sanin wanda ya kamata su zaba tun lokacin yakin neman, domin idan suka yi kuskuren zaben-tumun-dare, to za su ci gaba da zaman yin da-na-sani da cizon yatsa na tsawon shekaru hudu.

“Wato na zauna ne na yi nazarin irin kalamai da alkawurran da ‘yan siyasa muke yi domin cin zabe. Wasu batutuwan akwai su, amma ana murguda zance ko a canja ma’ana ko manufa da gangan a wurin yakin neman don kawai a ci zabe kuma a karkatar da hankulan jama’a. A karshe sai ka ga wadanda jama’a suka dora kan mulki, ba su biya masu bukatun da suka wajaba su biya masu ba.

“Ni littafi na ya karkata ne wajen wayar wa talakawa ‘yan Najeriya kai, bai karkata wajen goyon bayan ‘yan siyasa ba.

“Su fa ‘yan siyasa ‘yan yaudara ne. Dole sai sun yi yaudarar nan. Kamar mai neman aiki ne, wanda zai rubuta har abin da ba gaskiya ba ne dangane da shi, don dai kawai ya samu aiki, bukatarsa ta biya idan ya samu aikin.

">

“To ya rage ga masu zabe su sani cewa daga yanzu ba za mu sake aminta ko lamuntar mayaudara ba. Yaudarar ta isa haka nan. Daga wannan zabe zuwa wannan sai kyankyashe gurbatacciyar gwamnati ake ta yi duk bayan shekaru hudu.

”Ya ce, yana bukatar kungiyoyin wayar da kan jama’a su yi amfani da littafinsa wajen wayar wa jama’a kai a kan su daina zaben mayaudaran ‘yan siyasa. Daga cikin wasu lakanoni da ‘yan siyasa ke amani da su wajen yaudarar jama’a da karairayi, akwai: Yawan jama’a da addinanci da kudi da siyasar uban-gida da kabilanci da bangaranci da rikicin kabilanci da fadace-fadacen makwautan kabilu da kakaba wanda jama’a ba su so kan takara da dukiya da shahara da talaucin masu zabe da rashin gane inda aka dosa ga masu zabe, sai kuma amfani da tsarin tarayya.

Akwai kuma bambancin dan Kudu ko dan Arewa da kakaba tsarin karba-karba da dora matasa kan turbar dabanci da jagaliyanci da bijiro da ayyukan taimakon jama’a ga talakawa don a ja hankalinsu su zabi mai yi masu taimakon daga baya da amfani da fifikon ilmi ko fifikon dukiya da bambancin attajiri da fakiri da siyasar gado ko nuna fifikon asali na sarautar gargajiya.

Manyan ‘yan siyasa da dama na Jihar Kwara sun halarci taron kaddamar da littafin, wasu kuma sun tura wakilansu.

">

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

by Maryam Umar Said
August 4, 2021
0

Jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya sun mayar wa tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC) na ƙasar martani game...

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

by Abubakar Ismail kankara
April 4, 2021
0

UWAR JAM'IYYAR APC TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA AMSHI DR SURAJO YAKUBU BATAGARAWA YAU LAHADI 4/4/2021,,, ________________ Uwar Jam'iyyar Apc...

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

by Abubakar Ismail kankara
March 31, 2021
0

Hadimin gwanan yayi wannan bayani ne a wata hira da akayi dashi a yau laraba 31 ga watan mayu shekarar...

APC ba Ta isa Ta kwashe shekara 36 Tana Mulki ba – PDP

by Abubakar Ismail kankara
March 24, 2021
0

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi raddi kan kalaman da abokiyar hamayyarta APC mai mulkin kasar ta yi...

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

by Abubakar Ismail kankara
March 24, 2021
0

Shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta tsara yadda za ta ci gaba da...

A shirye nake na fice daga jam’iyar APC matukar masu yi min zagon kasa ba su hankalta ba__Ahmad Bola Tunibu ga APC.

A shirye nake na fice daga jam’iyar APC matukar masu yi min zagon kasa ba su hankalta ba__Ahmad Bola Tunibu ga APC.

by Abubakar Ismail kankara
March 6, 2021
0

Biyo bayan tambarin bincike da hukumar EFCC ta dasa akan jigo a jam’iyar APC, Ahmad Bola Tunibu ya yi magana...

Next Post
Zanyi kokarin samar da tsaro a Karamar hukuma Ta – Barista Esther

Zanyi kokarin samar da tsaro a Karamar hukuma Ta - Barista Esther

Addu’a Shugabanni Ke Buƙata Wajen Talakawa – Lawan

Addu’a Shugabanni Ke Buƙata Wajen Talakawa – Lawan

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In