Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce tana zargin Kamfanin sadarwar zamani na Twitter da munafunci bayan kamfanin ya goge wani bayani da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.
A wasu sakonni da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika a dandalin Twitter, ya ja-kunnen ‘yan bana-kwai da suke kokarin jawo sabon yakin basasa da su shiga taitayinsu kada allura ta tono garma.
Rahotanni sun bayyana cewar bayan an kai wa kamfanin Twitter kuka, sun goge maganar da shugaban kasar ya yi a ranar Talata ba tare da wani ɓata lokaci ba.
A martanin da ya bayar Ministan yada labarai na kasa, Alhaji Lai Mohammed, yana zargin kamfanin da rashin adalci. Alhaji Lai Mohammed yake cewa Twitter sun yi mursisi a lokacin da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake aika sakonnin da suke tunzura al’umma.
A cewar Ministan, Twitter ba ta ga dalilin goge sakonnin Nnamdi Kanu da suka yi sanadiyyar kashe ‘yan sanda da aka rika yi a yankin Kudancin Najeriya ba, sai rubutun mai girma Shugaban ƙasa. Haka zalika, Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna irin wannan son-kan a lokacin da aka yi zanga-zangar EndSARS wanda a karshe lamarin ya zama ta’asa.
Ministan yayi mamakin yadda kamfanin ke ganin akwai matsala a bayanin da shugaban kasar ya yi, ya ce gwamnati ba za ta zama sakarya ba. Ministan yake cewa:
“Wata kungiya ta na bada umarni ga ‘ya ‘yanta su kai hari a ofishin ‘yan sanda, su kashe jami’an tsaro, su kai farmaki a gidajen yari, a kashe gandurobobi, amma kuna cewa shugaban kasa ba zai iya magana domin ya nuna fushinsa ba?”