Mutane da dama, ciki har da wata mai juna biyu, sun rasu yayin da gobara ta tashi lokacin da suke ƙoƙarin kwasar fetur daga wata motar manfetur da ta yi hatsari a Dikko, Jihar Neja, kusa da Abuja, babban birnin tarayya.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar tankar fetur din ta fara ne lokacin da wasu mutane ke zubawa jarkokinsu da sauran mazubansu fetur daga tankar da ta faɗi.
Bugu da ƙari, an ce masu kwasar man sun girke injin wucin gadi na wutar lantarki a wurin, wanda ya haddasa gobarar.
Wani shaidar gani da ido ya ce mutane da dama sun rasu, amma ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa ransu ba. ‘Yan kwana-kwana na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar tankar fetur din har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X