Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa Kansilan gundumar Guringawa a cikin Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda kwanan nan ya nada mataimaka 18 a karkashin ofishinsa domin su taimaka masa wajen tafiyar da ayyukansa a bangarorin mabanbanta.
A wata takarda da mai taimakawa Gwamna na musamman akan harkokin siyasa, Hon. Muhammad Sani Tarauni ya aike wa Kansilan, Ganduje ya ce “Labari ya ishe mu game da namijin kokarin da ka yi wajen nada mataimaka 18 domin ganin ka samu nasarar gudanar da ayyukanka, da ciyar da yankin ka gaba. Na tabbata babu wani mutum mai irin matsayin ka da ya taba yin irin wannan abu da ka yi”
Gwamna Ganduje ya kara da cewa “Hakika samun mutum irinka a Jihar Kano babban cigaba ne ga demokradiyya. Mun san cewa babu wani tanadi da aka yi na irin wannan, amma ka dauki dawainiyar su cikin albashinka”.
Da karshe Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga takwarorinsa da sauran masu mulki da su yi koyi da halayen Muslihu Yusuf Ali don cigaban al’umma.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER