Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS) reshen jihar Kano ta bayyana cewa fursunoni 58 ne suka zana jarabawar kammala sakandire ta ƙasa (NECO) a shekarar 2025.
Kakakin hukumar a Kano, Musbahu Kofar-Nasarawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce fursunonin na ci gaba da zana jarabawar ne duk da kasancewarsu a cikin gidan yari.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta biya wa fursunonin kuɗin jarabawar domin ba su damar samun shaidar kammala karatunsu na sakandire.
Kofar-Nasarawa ya ce matakin ya nuna yadda gwamnatin jihar ke da ƙudurinta na tallafa wa fursunoni da nufin farfaɗo da rayuwarsu, ba kawai yayin zaman gidan kaso ba, har ma bayan sun kammala hukuncinsu.
A cewarsa, wannan dama za ta bai wa fursunonin damar samun cigaba a rayuwa, musamman ta fannin ilimi, wanda hakan na iya hana su komawa sabuwar laifi bayan sun fito.
KU BIYO MU A FACEBOOK