SHINKAFI, JIHAR ZAMFARA — Rikici mai tsanani da ya ɓarke tsakanin ɗan bindiga da aka fi sani da Bello Turji da kuma jami’an tsaro na sa-kai a Zamfara Civilian Protection Guard (CPG) ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 100 a kusa da kauyen Cida da ke ƙaramar hukumar Shinkafi.
Wani mazaunin yankin, Sa’idu Garba, ya shaida wa Jaridar Punch cewa ƴan sa-kai daga Zamfara da taimakon ƴan sa-kai na mai duguri wato (CJTF), sun ƙaddamar da wani hari a sansanin Turji ba tare da sahalewar hukumomin tsaro ba, da nufin kama shi kai tsaye—rai ko a mace.
An bayyana cewa wani tsohon ɗan bindiga da ya tuba, Bashari Meniyo, ne ya jagoranci harin.
“Sun tara kansu bisa jagorancin Bashari Meniyo, suka nufi sansanin Turji kai tsaye ba tare da sanar da jami’an tsaro ba,” in ji Garba. “Turji ya samu labari kafin su iso, sai ya tara fiye da mayaka dubun guda don kare kansa.”
Lamarin ya rikide zuwa faɗa mai zafi da aka shafe sa’o’i ana musayar wuta, inda aka kashe mutane da dama, ciki har da Bashari Meniyo da wasu daga cikin tawagarsa.
Wani mazaunin garin, Mohammed Sani, ya ce an ji karar bindigada da harbe-harbe da dama a ranar Litinin, kuma lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin.
“Mutane sun farka da karar bindiga, kowanne na neman mafaka, suna tserewa cikin daji domin tsira da rayuwarsu,” in ji shi. “Faɗar ta daɗe sosai ba tare da jami’an tsaro sun shigo sun kaw agaji ga yan sakai din ba.”
Garba ya bayyana takaicinsa kan rashin saurin daukar matakin hukumomin tsaro. “Da an zo cikin lokaci, da Bello Turji ya shiga hannun,” in ji shi.
Kokarin jin ta bakin jami’an tsaro ya ci tura, domin Lt. Col. Suleiman Omale, mai magana da yawun rundunar soji a jihar, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa ba.
Sai dai mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Mustafa Kaura, ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya ce bai da tabbacin adadin mutanen da suka mutu ba.
“Ina da tabbacin cewa lamarin ya faru, amma har yanzu ba ni da cikakken bayani kan yawan waɗanda suka rasa rayukansu. Ana gudanar da bincike,” in ji Kaura.
Rikicin dai ya ƙara jefa yankin cikin fargaba, inda al’umma ke ƙara rasa kwanciyar hankali sakamakon yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a sassan jihar.
KU BIYO MU A FACEBOOK