Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta sallami ma’aikata 27 a wani yunkuri na dakile zamba, cin hanci da rashawa, da sauran manyan laifuka masu alaka da su.
Mai magana da yawun hukumar, Musta Delete Oyewale, ya bayyana wa manema labarai cewa shugaban hukumar ya riga ya sanya hannu kan takardar sallamar ma’aikatan da suka tafka laifukan da suka hada da aikata zamba da cin amanar hukumar.
“Muna bin diddigin duk wani jami’in hukumar; babu wanda za mu kyale ya ci amanar wannan kasa,” in ji Oyewale.
Haka kuma ya bayyana cewa ana zargin wasu jami’ai da wawurar kudade da suka kai kimanin dala 400,000, tare da tabbatar da cewa za a gano wadanda ake zargi nan ba da dadewa ba.
Oyewale ya kara da gargadi ga masu amfani da sunan hukumar wajen damfarar mutane, inda ya bukace su da su tuba ko kuma su fuskanci hukunci mai