Daga: Muhammad Aminu Kabir
Hukumar Dake Yaƙi Da Ta’annuti Ga Tattalin Arzikin Ƙasa Cin Hanci Da Rashawa EFCC Ta Kama Jami’ai Biyar Na Hukumar Tattara Haraji Ta Jihar Katsina A Kan Zargin Satar Sama Da Bilyan Guda Na Naira….
Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annuti (EFCC) reshen Kano sun kama jami’ai biyar na hukumar tara kuɗaɗen Haraji ta Jihar Katsina bisa zargin karkatar da naira biliyan ɗaya da miliyan Ɗari Biyu da Chasa’in da Huɗu, da Dubu Ɗari Ukku da Talatin da Bakwai, da Ɗari Shidda da Saba’in da Shidda, da kobo Hamsin da Ukku (N1,294,337,676.53) mallakin gwamnatin jihar Katsina.
Waɗanda aka kama sun a hukumar tattara haraji haɗa sun hada da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da kuma Nura Lawal Kofar Sauri.
An kama su ne bayan samun ƙorafi daga gwamnatin jihar Katsina wanda ke zargin cewa waɗanda ake zargin sun yi wata hada-hada tare da karkatar da kuɗaɗen da suka kai N1,294,337,676.53 da aka ware wa jihar daga Ƙungiyoyin duniya irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Medicins Sans Frontiers, da Alliance for International Medical Action (ALIMA).
Bincike na farko da hukumar EFCC ta gudanar ya gano cewa Rabiu Abdullahi, tsohon Daraktan Tara kuɗaɗe kuma yanzu Sakatare na Dindindin na Hukumar, ya amince da buɗe asusun banki da aka yiwa laƙabi da suna “BOIRS” a bankin Sterling. an kuma naɗa Sanusi Mohammed Yaro, Daraktan Asusun kuɗaɗe, da Ibrahim M. Kofar Soro a matsayin waɗanda ke da damar sa hannu kan asusun. Bayan haka, an yi amfani da wannan asusu wajen karkatar da kuɗaɗen zuwa ga babban mai cin gajiyar kuɗaɗen, NADIKKO General Suppliers, wani kamfani mallakin Nura Lawal Kofar Sauri, mataimakin darakta a ɓangaren horarwa da jin daɗin ma’aikata na hukumar.
Bincike ya kuma gano cewa Nura Lawal da kamfaninsa “NADIKKO” ne suka zama hanyar karkatar da kuɗaɗen da aka sace. An gano cewa an tura waɗannan kuɗaɗen zuwa asusun bankuna daban-daban mallakin wanda ake zargi.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar ta EFCC reshen Kano. Za a gurfanar da su a gaban ƙuliya da zarar an kammala bincike cewar hukumar ta EFCC.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X