Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan ƴada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce hukumomin kamfanin Twitter sun tuntuɓi gwamnatin tarayya domin tattaunawa kan matakin dakatar da amfani da shafin da gwamnatin Buhari ta yi.
Ministan ya shaida wa manema labarai hakan ne bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba cewa kamfanin Twitter na neman “tattaunawa mai ƙarfi” don warware matsalar da ta kai ga dakatar da ayyukansa a Najeriya.
“Shugabannin gudanarwar Twitter sun tuntuɓi gwamnati a ranar Laraba,” in ji Lai Mohammed.
A ranar juma’a gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter kan zarginsa da bayar da dama ga waɗanda ke barazana ga ɗorewar Najeriya.
Dakatarwar na zuwa bayan kamfanin ya goge ɗaya daga cikin sakwannin shugaban Najeriya inda ya ke barazanar ɗaukar mataki kan masu da’awar ɓallewa daga Najeriya.
An kuma ambato Lai Mohammed na cewa, dgaa yanzu duk wani kamfanin kafar sadarwa sai yi rijista tare da ba shi lasisi kafin ya fara ayyukansa a Najeriya.
KU BIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER