Dalilin da yasa ƴan bindiga ba zasu ajiye makamai ba – Gumi
Shahararren Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ba lallai yan bindigan daji su ajiye makamansu idan har basu samu tabbacin aminci da tsaro ba.
Gumi ya bayyana haka ne yayin wani taro daya gudana ta yanar gizo wanda cibiyar nazarin dokoki da siyasa ta kasa ta shirya, inji rahoton Daily Trust.
Gumi ya dage lallai sulhu ne kadai zai kawo karshen hare haren yan bindiga, saboda a cewarsa akwai mummunan hatsari a kyale matasa marasa ilimi su waye da amfani da miyagun kwayoyi.
“Babu wanda zai halasta miyagun ayyuka, abinda muke cewa shi ne abinda muka gani a dazuka yaki ne na kabilanci tsakanin mutanen dake dazuka da makwabtansu dake kauyuka da rugage.
“A lokacin da makiyayi yake ganin yana da matsaloli, amma babu wanda ke sauraronsa, daga nan ne ya fara daukan makamai. Saboda haka da muka je muka sauraresu, sun bayyana shirinsu na tattaunawa.
“Sun fada mana matsalolinsu, kuma sun bayyana shirinsu na komawa cikin al’umma, don haka ban ga dalilin da zai sa ba za mu tattaunawa dasu ba. Basu da wani nau’in ilimi kowanne iri.
“Ta yaya kasar dake da azamar tabbatar da tsaro za ta bar matasa kara zube ba tare da ilimi ba, har su samu wayewa da amfani da miyagun kwayoyi da makamai?
“Ta yaya zamu tarwatsasu, mu basu kulawa, idan har bamu basu tabbacin tsaron rayukansu a cikin jama’a ba, toh lallai babu yadda zasu ajiye makamansu.” Inji shi.
Daga karshe, Malamin yace shi yasa yake neman a musu afuwa kamar yadda aka yi ma tsagerun Neja Delta afuwa