A day dai lokacinda masana kimiya da kuma ma su kere-kere ke fantsama wajen kirkiro ababen more rayiwar dan adam cikin sauki da walwala, wani matashi kuma kwarare a fannin kera kekunan hawa Malam Umar Yusuf dan asalin jahar Borno ya kera keken zamani mai amfani da inji don saukaka zirga-zirga.
Malam Umar wanda ya samu shaidar difloma a fannin fasahar noma a kwalejin aikin gona ta Mohammet Lawan da ke jihar Borno, ya bayyana wa Jaridar Daily Episode cewa ya fara sana’ar facin ne a shekarar 2012 tun yana dalibi.
A cewar shi, daka bisani, ya koyi kanikancin keken har na tsawan shekaru uku, wanda a dalilin hakan ya samu damar samun kwarin gwiwa dakuma basirar gano kirkira keken zamanin da Allah yahore ma sa.
“Na kasance mai shaawar kirkira da kere-kere, anma na fuskanci kalubale da dama, musanman kasancewar na fito daga yankin da ke fama da matsalar tsaro da ingantacciyar wutar lantarki, wanda hakan ya zame mani togaciya tun lokacin da ina bakaniken keke”.
“Amma duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba, na cigaba da kokarin ganin burina na kera kekuna ya zama gaskiya tare da kokarin samarwa mutanen jahar Borno da alu’uma mafita wajen zirga zirga musanman wadanda rashin tsaro ya tilastawa dena amfani da babura sakamakon dokar hana amfani da babura a yankunan dake fuskantar kalubalen rashin tsaro”.
Ya kara da cewa “Nayi kokarin cigaba da karatu amma Saboda matsalar rashin kudi hakan bai yiwuba. Wanda daka bisani, bayan shekaru uku ina koyon kanikancin keke na fara kera kekuna, wanda a yanzu haka na kera kekuna da dama”.
Ya zuwa yanzu, daka sadda na fara kera kekuna a farkon shekarar 2017, na kera kekuna da adadinsu ya kai a kalla guda 57, kuma na sayar da su, daga cikinsu akwai kekunan hawa guda 32, kekunan daukar kaya 7, kekunan guragu 7, kekuna zamani masu amfani da inju guda 4, da Na guragu na musanman guda 2.
Yabo da nake samu daga wajen jama’a dakuma masu siyan kekunanan nawa na karamin karfin guiwa matuka, don ina jin dadin hakan a koda yaushe.
Sai dai duk da cewa yanzu na inganta kekuna zuwa masu amfani da injina da kuma karin inganci, a shirye nake da yin fiye da haka, sai dai akwai kalubalen rashin kudi da nake fuskanta, wanda kuma ina fatan samun tallafin da zai taimakamin wajen bunkasa wannan sana’ar da nake fatan rage zaman banza da kuma samar da aikin yi ga alumma.
Kubiyomu A Facebook, TWITTER, INSTAGRAM, LINKEDIN & YOUTUBE