Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rusa majalisar zartarwa ta jihar da ta hada da kwamishinonin sa da kuma korar sakataren gwamnatin jihar (SSG), Barista Muhammad Aliyu-Ubamdoma.
Jaridar Weekend Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa na musamman da aka yi a gidan gwamnati dake garin Lafia a ranar Juma’a jim kadan bayan tafiyar mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar domin kaddamar da aikin. wasu ayyuka a jihar.