Akalla mutum 39 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar Coronavirus a birnin Shanghai na China mai hada-hada a ranar Asabar.
Kafar yada labarai na BBC sun ruwaito cewa wannan shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun tsaurara dokar kulle makonni hudu da suka gabata.
Birnin Shanghai mai al’umma miliyan 25 yanzu haka na fama da barkewar wannan annoba mafi girma a China kawo yanzu.
Ana ci gaba da daukar matakai masu tsauri, da kwashe mutane daga gidajensu domin yi feshi.
Sannan a Beijing, jami’ai na gargadi kan barazanar da cutar da ke yaduwa cikin gaggawa ke haifarwa.