Babban bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa,ba zai kara baiwa bankin NIRSAL kudi ba a rabawa manoma har sai an warware matsalar basukan da aka bayar a baya.
Hakan na zuwane yayin da ake zargin cewa an tafka rashawa da cin hanci yayin bayar da bashin da aka rika yi a baya.
Daily Episode ta bayyana cewa ana zargin shugaban bankin, Aliyu Abdulhamid da rashawa da cin hanci sosai, lamarin da shine ya jawo CBN ta dauki wanan mataki.