Wani dan Majaliisa Mai wakiltar mazabar Bogoro a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Honarabil Musa Nakwada yace Gina Mutunan Karkara shine wakilcin shi zai maida hankali,don ganin sunci gajiyar Mulkin Dimokuradiya ,Kamar Gina Gadaje, Kwalbatoci,da Samar Musu da hanya don Fitar da Kayayekin amfaninsu zuwa Birane don Sai da su cikin riba,
Honarabil Nakwada ya baiyana haka ne a zauren Majalisar yau a Jihar Bauchi, ya Kara dacewa “Mutanen na da nake wakilta suna cikin wani mawuyacin hali na Rashi hanya a hanlin yanzu sakamakon Zabtarewar gada a yankinsu wanda hakan yasa koda wani hali Mace mai Ciki ,take Ciki na Nakuda baza’a lya wucewa da lta ba don kaita Asibiti ba don karbar haihuwarta ba,
Dan Majalissar ya Kara da cewar halin ya nuna cewar lalle akwai bukatar muna zuwa Mazabunmu don ganin halin da suke ciki, daga karshe yayi kira da Shugaban Majalissar daya mika wannan bukata tashi ga Kwamiti na Aiyuka da kuma mika Koken nasu don ganin Gwamnatin Jihar ta kawo musu dauki a yan kunansu ta hanyar Gida musu Gadoji don rage wahalhalun da suke fuskanta musamman lokacin damuna,
Shi kuwa Honarabil Tukur Ibrahim Mai wakiltar Toro/ Jama’a a Majalissar dokokin jihar Kudiri ya kawo na ganin sakawa reshen Kwalejin aikin Goma ko kuma sakawa Ginin Hukumar Zartarwar Jami’ar Jihar Bauchi, Sunan Babban Sakataren Kula da manyan Makarantu Farfesa Suleiman Elias Bogoro Sunansa wanda ya baiyana cewar zai karawa na baya Kwazo na ganin sun samarwa Jihar cigaba lura da cewar anyi irin haka abaya inda ya anbaci Sunan Shahararrun gwaraza da aka sama sunayensu Kamar su Tatari Ali,Sa’adu Zungur ,Abubakar Tafawa Balewa da dai sauransu,
Bayan gabatar da wan nan Kudiri ne a Karatu na daya Kakakin Majalissar dokokin Honarabil Abubakar Suleiman ya daga zamanta zuwa makon gobe.
Daga Abdullahi Alhassan, Jihar Bauchi