Shugaban kungiyar dake kare muradun yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo ya bayyana cewa, ko kadan Shugaba Buhari ba zai mikawa Tinubu Mulki ba.
Yace idan Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa ta APC, ba zai kai labari ba. Yace kuma dama can yasan ba zaman gaskiya tsakanin Tinubu da shugaba Buhari.
Yace Dukan biyun yaudarar Juna suke. Ya kuma jawo hankalin shuwagabannin yankin da su mayar da hankali wajan ganin an canja Fasalin kasa inda yace in banda Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, Tinubu da Osinbajo sun yi shiru akan batun.