Yayin da Boko Haram ke ci gaba da kai hare-haren kashe-kashe da rushe-rushe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, akalla fasinjoji tara sun rasa rayukansu a kauyen Mairari, da ke ƙaramar hukumar Guzamala a Jihar Borno.
Jaridar Daily Episode ta tattaro cewa ‘yan Boko Haram sun dasa boma-boman IEDs a wajen tashar mota ta kauyen, inda boma-boman suka tarwatse suka hallaka fasinjojin da ke jiran hawa mota, lamarin da ya jikkata wasu da dama.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya la’anci harin, yana mai bayyana shi a matsayin aikin rashin imani da takaici.
A cewarsa, “’Yan ta’addan sun riga sun mamaye gaba ɗaya ƙaramar hukumar Guzamala a halin yanzu, ko da yake ina roƙon rundunar soji da ta kawo dauki domin dawo da zaman lafiya a yankin.
“Ina cikin matuƙar bakin ciki da ɓacin rai kan rasuwar wasu mutane tara daga cikin al’ummata, waɗanda suka mutu sakamakon fashewar IED da aka dasa a kauyen Mairari. Wannan abin takaici ne ƙwarai, ina kuma roƙon Allah ya jikan su da Aljannatul Firdaus, ya kuma ba wa waɗanda suka jikkata waraka cikin gaggawa — domin a yanzu suna karɓar magani a asibitocin Monguno da Maiduguri.”
Lawan ya ƙara da cewa, “Kauyen Mairari da abin ya faru, na ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyuka da aka taɓa sake maido da zama a cikinsu sau biyu ta hanyar ƙoƙarin fararen hula a Guzamala, amma a yau an sake ruguza shi sakamakon dawowar hare-haren Boko Haram/ISWAP.
“Za ka ga yadda mutanen nan suke da jajircewa, domin mafi yawan waɗanda ke zaman gudun hijira a Maiduguri, Monguno da Guzamala na yawan dawowa Mairari domin kasuwanci da harkar noma.
“Amma abin takaici, a yau waɗannan ‘yan ta’adda sun yi nasarar dasa boma-boma a tashar mota ta kauyen, inda ta fashe ta hallaka mutane da dama masu laifi, tare da jikkata wasu da dama da suke fama da munanan raunuka.”
A cewarsa, “A wannan lokaci na tsaka mai wuya, yana da matuƙar muhimmanci a mayar da hankali wajen kwato Guzamala daga hannun ‘yan ta’adda. Duk da cewa mun san sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, da dakarunsa suna bakin kokarinsu wajen yaki da ‘yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas — kwato Guzamala zai zama babban nasara da ya kamata a fifita.”
A lokacin da Daily Episode ke wallafa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma ba dangane da lamarin.
KU BIYO MU A FACEBOOK