Daga Bello Usman, Kano.
Sanarwar da ofishinsa ya fitar ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce tsohon shugaban da iyalansa na nazari kan matakin dauka na maganin cutar tare da kwararrun likitoci.
Likitocin sun ce duk da munin nau’in kansar amma sauyin da ake samu na jikin mai dauke da ita, ba zai hana yin maganinta da saurin karbar sauyi ga jikin dan adam ba.
A cewar sanarwar, “Mr Biden ya je asibiti domin yi masa gwaje-gwaje sakamakon matsalar da ya ke samu wajen yin fitsari, anan ne likitoci suka gano akwai wani kullutu a marainarsa, kuma bayan karin wasu gwaje-gwajen aka tabbatar ya kamu da mummunar nau’in cutar kansar mafitsara da ta fara yaɗuwa zuwa kashinsa”.
Tuni jiga-jigan jam’iyyar Democrat a sassan Amurka suka fara wallafa sakonnin karfafa guiwa, inda shima Shugaba Trump ya ce bai ji dadin labarin halin da Biden ke ciki ba, ya na kuma yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.
Shima tsohon shugaban Amurka kuma na hannun daman Mr Biden, Barrack Obama, ya wallafa a shafinsa na X cewa shi da maidakinsa Mixchelle na tare da iyalan Biden a irin wannan lokaci.
A cewar Obama, “Babu wanda ya yi namijin kokari domin ganin an samar da maganin cutar kansa kamar Biden, na kuma yi imanin zai cinye wannan jarabawa adan haka muna yi masa addu’ar samun sauki”.
Mr Biden mai shekara 82 a duniya ya sauka daga mukaminsa a watan Junairu, kuma shi ne shugabn Amurka da ya fi sauran shekaru a tarihi.
KU BIYO MU A FACEBOOK