Shugaban Amurka, Joe Biden da Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu sun tattauna ta waya a daidai lokacin da ake ci gaba da zura ido dangane da batun tsagaita wutar Gaza – a makon ƙarshe na Biden a matsayin shugaban Amurka.
Alamu na nuna cewa Isra’ila da Hamas sun fahimci juna kuma suna ci gaba da tattaunawa duk da cewa akwai ƴan abubuwan da suka ƙi yarda da juna a kai.
Fadar White House ta ce Biden ya tattauna kan “muhimman abubuwan da za su iya sauya yanayin da Gabas Ta Tsakiya ke ciki” tun bayan tsagaita wuta da Hezbollah a Lebanon, da faɗuwar gwamnatin Assad a Syria da kuma gurgunta ƙarfin Iran a yankin na Gabas ta Tsakiya.
Ofishin firaiminista Netanyahu ya ce ya sanar da Biden kan umarnin da ya bayar ga manyan masu shiga tsakani a Doha “domin su tabbatar da sakin mutanen da ake garkuwa da su”.

Yayin wata tattaunawa ta waya wanda ita ce irinta ta farko da aka bayyana tun watan Oktoba, Biden “ya nanata bukatar gaggawa ta kammala yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma ƙara yawan kayan jin ƙai”.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Netanyahu ya aike da babbar tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka haɗa da daraktocin ƙunigyar leƙen asiri ta Mossad da tsaron ƙasar, Shin Bet domin wucewa gaba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Qatar da AMurka da Misra ke jagoranta.
Kafafen watsa labaran Isra’ila sun rawaito cewa Netanyahu ya gana da jami’an gwamnatinsa da ke adawa da shirin tsagaita wutar domin ya lallaɓe su ka da su yi murabus.
Ministan harkokin wajen Burtaniya, David Lammy ya gana da Benjamin Netanyahu a Jerussalem domin tattauna cigaban da ake samu dangane da yarjejeniyar.
A ranar A sabar ne wakili na musamman da zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump a Gabas ta Tsakiya ya gana da Benjamin Netanyahu kan yarjejeniyar kafin ranar 20 ga watan Janairu – ranar da za a rantsar da Trump ɗin.
A baya dai mista Trump ya ce “za a yi ɓatacciya” idan dai har ba a saki waɗanda ake garkuwar da su ba kafin ya sake kama aiki.
A ranar Alhmis ɗin da ta gabata ne sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce “yarjejeniyar na dab” da kasancewa kamar yadda muke fata kafin Trump ya kama aiki. Duk wata yarjejeniya da za a cimma to za ta zama bisa doron tsarin da Joe Biden ya shaimfiɗa.
Duk da cewa ana aiki tuƙuru kan yarjejeniyar, amma rashin cikakken bayani kan wasu muhimman abubuwa da suka haɗa da ko yarjejeniyar ta farko za ta ɗore zuwa tsayar da yaƙin baki ɗaya sannan ko Isra’ila za ta amince da janye sojojinta daga Gaza baki ɗaya.
Sai dai kuma wakilin jaridar Isra’ila ta The Economist, Anshel Pfeffer ya ce ba ya tsammanin za a iya cimma wata yarjejeniya cikin gaggawa.
To amma ya ƙara da cewa burin Isra’ila da Hamas ne ganin sun cimma yarjejeniyar kafin Trump ya kama mulki.
“Akwai fargaba tare da Hamas cewa Trump ka iya bai wa Netanyahu damar ƙaddamar da muggan hare-haren da a baya ba su yi ba.”
“Dukkan ɓangarorin sun nuna gajiya, sun wahala sosai.”
Isra’ila ta ce har yanzu dai akwai ragowar waɗanda Hamas ke garkuwa da su a Gaza su 94, kuma ana tsammanin 34 daga ciki sun rasu tare da ƙarin mutum huɗu da Hamas ɗin ta kama gabanin yaƙin inda biyu daga cikinsu suka mutu.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X