Addinin musulunci yayi tanadin yadda ake gudanar da sayisa. Watau As-siyasa-ash-shar’iya, yadda ake naɗa shugaba, da kuma yadda shugaban ya kamata ya tafiyar da shugabancin na tsare addinin da rayukka da dukiyar jamaa, da mutuncinsu da zurriyarsu ta hana Zina. Wannan shine Siyasar dake cikin Addinin Muslunci.
To amma cewa babu ‘addini ckin siyasa’ a zamanance, ana nufin watau baa anfani da addini domin neman mulki kawai ba domin a aiwatar da hukunce-hukuncen shari’ar musulunci ba. Wannan shine ci da addini (al-aklu biddin). Watau a yi anfani da sunnan addini domin cimma wani guri na duniya. Acikin wani hadisi wanda Albukhari da Muslim suka ruwaito daga Umar dan khattab – radiyallahu ‘anhu- wanda yace yaji Manzon Allah –Sallahu ‘alaihi Wa Sallam- yana cewa:
»إِنَّمَا الْأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى دُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوْ إِلَى امْرَأَةٍ ينكحها، فهجرته إلى ما هاجر إليه«
Lalle ayyukan addini da niyarsu kawai ake karba, kuma lalle ga kowane mutum yana da abunda yayi na aiki gwargwadon niyarsa kawai. Saboda haka duk wanda hijirasa ta kasance domin samun duniya ko domin mace ya aureta, to hijirasa tana ga abunda yayi hijira zuwa gareshi”
Wanda yayi siyasa da addini domin samun duniya, Toh siyarsa ba ta addini bace kuma babu ladar wannan siyasar domin ba don ayi hukuncin Allah da ita ne ba sai dai mallakar mutane da garadi na duniya.
Tarihi ya tabbatar da yadda Allah –madaukaki – Yake halaka mutane idan suka kasance azzulami. Allah Yace:
﴿وَكَمْ قَصَمْنَا مِنْ قَرْيَةٍ كَانَتْ ظَالِمَةً وَأَنْشَأْنَا بَعْدَهَا قَوْمًا آخَرِينَ﴾ [الأنبياء: 11]
Maana:
“Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta. “
Saboda haka mubar yaudarar Allah da Mutane da addini cikin siyasa, muyi siyasar da zata taimakawa addini kuma ta tsare rayuka da dukiyar jamaa, da mutuncinsu da zurriyarsu ta hanzar hana sata da zina da tsayar da aƙidah da sallah.
Allah Ya shiryar damu, Ya bamu shugabanni Na ƙwarai Kuma Ya bamu zaman lafiya. Amin
Kubiyomu A Facebook, TWITTER, INSTAGRAM, LINKEDIN & YOUTUBE