">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Thursday, October 16, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Bama-baman Lakurawa Ne Suka Kashe Mutane A Silame Ba Harin Sojoji Ba – Sojoji.

by Abubakar Ismail kankara
December 29, 2024
in Sport Stories, Uncategorized
0
Bama-baman Lakurawa Ne Suka Kashe Mutane A Silame Ba Harin Sojoji Ba – Sojoji.
Share on FacebookShare on Twitter
">

RelatedPosts

Majalisar Wakilai Za Ta Tattauna Kan Kudirin Gyaran Haraji

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

">

Rundunar sojin Najeriya ta ce bama-baman da Lakurawa suka ajiye a ƙauyukan da sojojin suka kai wa hari ne suka kashe mutanen gari, ba hare-haren da sojojin suka ƙaddamar ba.

A ranar Laraba da safe ne aka samu rahotonnin hare-haren jiragen sojin Najeriya a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.

Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce sojojin ƙasar ne suka kai harin bisa kuskure, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 10, wani abu da gwamnan ya danganta da ƙaddara.

To sai dai cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Manjo JanarEdwar Buba ya fitar ya ce ba harin sojojin ne ya kashe mutanen ba.

Ya ce kafin kai harin, sai da sojojin suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanar da cikakken bincike ta hanyar tattara bayanan sirri, sanna suka tabbatar da cewa Lakurawa ne ke karakainarsu a yankin.

”Sannan jirginmu ya ƙaddamar da hare-hare kan wuraren da muka tabbatar da cewa na Lakurawa ne da misalin ƙarfe 6:00 na asubahin ranar 25 ga watan Disamba, ta hanyar amfani da ƙananan makamai domin taƙaita ɓarnar da hare-haren za su haifar,” in ji Manjo Janar Edwar Buba.

”Kuma sun tabbatar mana cewa hare-haren sun yi nasara, domin sun lalata maɓoyar Lakurawan, tare da ‘yar ƙaramar ɓarna a ƙauyen. Haka kuma sojojinmu na ƙasa sun zanta da mutanen ƙauyen inda suka tabbatar musu cewa akwai Lakurawa a inda aka kai harin,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa hare-harenmu sun yi nasara wajen kashe Lakurawa a yankin tare da lalata muhimman abubuwan da Lakurawan ke amfani da su ciki har da makamansu.

”Don haka faɗawar harin kan rumbun makaman Lakuwarar ya haifar da wasu ƙarin fashe-fashen bom a wurare daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10, kuma muna kan bincike domin tabbatar da cewa ko suna cikin masu taimaka wa Lakurawan ko akasin haka,” a cewar sojojin na Najeriya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen yankin sun tabbatar musu cewa Lakurawa na gudanar da harkokinsu a yankin

">
Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Kan Kudirin Gyaran Haraji

Majalisar Wakilai Za Ta Tattauna Kan Kudirin Gyaran Haraji

by Abubakar Ismail kankara
February 12, 2025
0

Majalisar wakilai za ta ci gaba da muhawara kan kudirin gyaran haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar...

Gobarar Tankar Fetur

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Mutane da dama, ciki har da wata mai juna biyu, sun rasu yayin da gobara ta tashi lokacin da suke...

harin jiragen Sojin

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Iyalan waɗanda harin jiragen Sojin saman Najeriya ya rutsa da su a Zamfara sun nemi gwamnati ta biya su diyya...

Asusun Bai Ɗaya

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa, daga ƙarshen watan Janairu, dukkan kananan hukumomi a Najeriya za su fara karɓar...

Murar Tsuntsaye

Kano Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Cutar Murar Tsuntsaye

by Abubakar Ismail kankara
January 17, 2025
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk...

Hukumar Tattara Haraji

EFCC Ta Kama Jami’an Haraji 5 Kan Satar Biliyan 1.2 a Katsina

by Abubakar Ismail kankara
January 14, 2025
0

Daga: Muhammad Aminu Kabir Hukumar Dake Yaƙi Da Ta'annuti Ga Tattalin Arzikin Ƙasa Cin Hanci Da Rashawa EFCC Ta Kama...

Next Post
Mutum 179 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama

Mutum 179 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In