Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon fashewar wani abin fashewa a wata makarantar Islamiyya da ke yankin Kuchibuyi, karamar hukumar Bwari a Abuja, babban birnin kasar.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Litinin, lokacin da wasu mutum uku suka kai ziyara ga shugaban makarantar, Mallam Adamu Ashimu.
“Binciken farko ya nuna cewa mutanen ukun ne ake zargi da kai abin fashewar zuwa makarantar. Abin ya fashe ne a farfajiyar makarantar, inda mutum biyu suka mutu nan take,” in ji sanarwar.
Wata mata mai sayar da kayayyaki da kuma ɗaya daga cikin mutanen ukun sun samu munanan raunuka, kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti.
Rundunar ta kara da cewa an tsare Mallam Adamu Ashimu domin amsa tambayoyi yayin da bincike ke ci gaba, kuma za a fitar da cikakkun bayanai nan gaba.