A yayin da ake ci-gaba da shirye-shiryen bukukuwan babbar Sallah, Hukumar dake hana sha da Fataucin miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kasa reshen jihar Kano, ta sami nasarar dakile hada-hadar Kwaya da sauran kayan maye a sassan jihar.
Kakakin rundunar na jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta aiko wa GTR Hausa, inda ya ce sun kama mutane 36 kan zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi a Makabartar Dan’agundi, Kwari, Kofar Na’isa da kuma Kano Line.
Kayan da aka kama sun hadar da tabar Wiwi, Sukudayin, Diazepam, Sholisho, da sauran kayan maye.
A ƙarshe sanarwar ta ce Kwamandan hukumar na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, ya ce sumamen na nufin tabbatar da tsaro da ingantacciyar rayuwa a yayin bukukuwan babbar Sallah a Kano.