Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaro da su zakulo ’yan ta’adda tare da masu daukar nauyinsu a duk inda suke, don gamawa da su, yana mai cewa, ba zai kara lamuntar irin mummunan halin da suke jefa talakawan Nijeriya ba.
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, wanda shi ya yi wa jawabin ga manema labarai a karshen taron tare da shugabannin tsaro, ya ce, Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa, ba zai kara lamuntar irin halin da ’yan fashi da masu satar mutane ke cigaba da jefa al’umma ciki ba.
Monguno ya ce, shugaban yana tsammanin sojojin kasar za su kasance masu himma maimakon yin martani.
Ya kara da cewa, Shugaba Buhari ya kuma ce su dage akan duk shawarar da aka amince da ita a taron Majalisar Tsaro ta kasa da aka gudanar a watan jiya, ciki har da hana ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama, da fatan kuma za’a ci gaba da aiwatar da su har zuwa lokacin da za a kara shawo kan lamarin rashin tsaro a kasar.
Munguno ya ce: “Bayan ganawa da gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, Shugaban ya yanke shawarar kiran taron gaggawa da shugabannin tsaro da na kungiyoyin tsaro.
“Kafin wannan taron, ya kuma gana da Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kan batutuwan da ke da nasaba da halin rashin tsaro a kasar. “Taron na yau ba ganawa ce mai tsayi sosai ba, amma Shugaban ya duba wasu batutuwa da aka gabatar masa a cikin mako guda da ya gabata.
“Shugaban, musamman, ya jaddada cewa, cikakken rahotannin da ya samu daga Babban hafsan hafsoshin tsaro da shugabannin hafsoshin, bayan nadin da aka yi musu kwanan nan, ya haskaka bukatar da yake da ita na zurfafa bincike kan wasu bangarorin da ya kamata a kula da su.
“Akwai alamar kwazo kwarai da gaske game da yadda sabbin hafsoshin sojojin suka fara aikinsu, tare da duk wata ziyarar aiki da suka kawo a sansanoninsu, inda suka sami damar yi wa sojojin jawabi, duba abubuwan da suke bukata nan da nan suka zo. tare da bada shawarwari kai tsaye, matsakaici da dogon lokaci.
“Shugaban zai duba wadannan abubuwa da gaggawa da suke bukata, amma yana matukar farin ciki cewa daga abin da ya karba daga babban hafsan, yanzu akwai sabon karfi, sannan akwai wasu shirye-shirye daga bangaren duk domin aiki tare, haka kuma suna aiki kafada da kafada da kungiyoyin leken asiri. ”
NSA ta kara da cewa: “Game da batun satar mutane da fashi kuwa, wannan barazanar har yanzu tana ci gaba, musamman a shiyyar Arewa maso Yamma da shiyyar Arewa ta Tsakiya. “Shugaban kasa ya kasance mai karfin gwiwa, ya bayyana karara cewa dole ne a kawo karshen wannan matsalar amma ta amfani da hanyoyin da aka horar da sojojin da za su yi aikin.
“Shugaban kasar ya kuma bayyana a sarari ga masu hankali da masu gudanar da aiki cewa aikin farko shi ne gano shugabannin wadannan barayin, masu satar mutane tare da fitar da su, don dawo da karfin gwiwa a wadannan yankuna.
“ Haka zalika, shugaban kasar ya ce ba zai kara yarda da ci gaba da zama a halin da ake ciki ba, ta yadda ‘yan bindiga da masu satar mutane ke tsara al’amuransu kuma su tafiyar da shi, wannan ba abu ne da za’a lamunta ba.
“Ya kuma bayyana aniyarsa ta samar da dukkan abubuwan da sojojinmu ke bukata domin kawar da wadannan masu aikata laifukan. “Dole ne a taka musu birki da su tare da duk rashin tausayin da suke nunawa ta hanyar bayar da goyon baya da hadin kai da karin kwarin gwiwar su za a hukunta su.
Ya kuma bayyana cewa ba za a samu daidaito a cikin duk abin da Majalisar Tsaro ta kasa ta riga ta shimfida ba har sai an dawo da al’amuran yau da kullum.