Hadimin gwanan yayi wannan bayani ne a wata hira da akayi dashi a yau laraba 31 ga watan mayu shekarar 2021.
A locacin da ake fira da Hadimin gwamana masari, Alh. Sabo Musa Hassan Katsina a wani shiri me suna Babbar magana na gidan radio vision FM katsina.
Dan jaridar yayima sabo musa tambaya kan maganar da shugaban rikon na jamiyyar Apc na kasa kuma Gwamnan Jihar yobe kan cewa Apc sai tayi shekara 32 tana mulkin Nigeria
Sai Sabo Musan yace “Bai kamata shugaban jamiyyar Apc ya fadi wanan maganar ba a matsayinsa na musulmi, domin Wanan shiga hurumin ubangiji ne Allah kadai yasan lokacin da Apc zatai tana mulki, har ya kawo Ayar Alkurni mai tsarki: “Allah shi ke bada mulki ga wanda yaso kuma a lokacin da ya so”
Kamata yayi shugaban jamiyar APC Mai mala Buni Yace, APC zata dade tana mulki amma kada ya fadi shekaru saboda fadin shekaru shiga hurumin Allah ne