Sabbin rahotannin dake fitowa kan matarnan data kashe zargin ta kashe sabuwar amaryar mijinta sannan ta konata a jihar Naija na cewa a baya ma ta taba yin hakan.
Ana zargin Amina Aliyu da kona ‘ya’yan kishiyarta 2 a shekarar 2018. Mijin matar, Aliyu Abdullahi Dayi ne ya bayyana haka.
Yace abinda ta yi yanzu ya alamta masa cewa itace ta kashe ‘ya’yansa 2 a baya da suka mutu a wata gobara me cike da sarkakiya, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake bayyana yanda lamarin ya faru, Dabi yace, baya gida amma aka kirashi aka sanar dashi lamarin, dan hakane yayi gaggawa ya koma gidan, yana zuwa ya tarar da abinda ya faru.