Wasu daga cikin jami’an Katsina Community Watch Corps (C-Watch) sunyi harbin uwa da wabi da harsasai a Mabai, karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda suka bar mutane fiye da 30 da raunuka, da jinya mai tsanani a asibitocin Katsina, Kankara da Malumfashi.
Lamarin ya fara ne lokacin da wasu daga cikin jami’an C-Watch din suka nemi yima wa wani matashi mai suna Mutaka Adamu wanda aka fi sani da Bamba, aski sakamoakn ya tara suma yayin bukukuwan Sallah a garin Mabai ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025.
A cewar wanda abun ya faru a gaban sa mai suna Aliyu Usman Mabai, “jami’an sun tare Bamba suka ce dole sai sun aske masa gashin kansa bisa dalilin da suka bayyana a matsayin wani bangare na dokar kula da aka basu. Amma matashin ya ki yarda, inda ya baiyana masu cewa bai aikata wani laifi ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Wasu dattawa a yankin sun shiga tsakani, inda suka roki jami’an su bar Bamba saboda tara suma ba laifi ba ne a shari’ar Musulunci ko al’ada.”
Bayan lokaci kadan, jami’an suka dawo suka kama Bamba a wata makarantar firamare. “ inda sukayi masa duka har sai da ya fita hayacinsa. ” in ji Aliyu.
Bayan al’ummar yankin sun ji yadda aka daka Bamba, matasa da dama suka fusata, suna tambayar dalilin da ya sa aka yi masa haka.
Daka bisani sai matasa suka fara cewa bamu yard aba inda har suka fara yima jami’an ihu suna cewa “bamayi, bamayi”.
Sai kawai jami’an suka bude wuta, inda suka harbi mutane da dama ciki har da mata da yara, wasu ma suna cikin gidajensu lokacin harbin.
Sojojin da ke zaune a Mabai ne suka zo inda daka bisani suka kwantar da tarzoma tare da taimaka wa wajen daukar masu rauni zuwa Asibitin Gwamnati na Kankara. Inda daka bisani aka kai wasu asbitin a katsina, malunfashi da kuma bakori sakamokon munin raunin da suka ji.
Alhaji Adamu Mamman, mahaifin Bamba, ya bayyana cewa lamarin abin bakin ciki ne. “A lokacin da muke fama da rashin tsaro, ba dace irin wannan abu ya faru ba. A daidai wannan lokaci, ya kamata a mayar da hankali wajen yaki da ‘yan ta’adda da barayin daji.”
Ya ci gaba da cewa, “Jami’an C-Watch sun so hana bikin Sallah da ake yi duk shekara a unguwarmu. Amma matasa suka ki amincewa. Sai suka ce wai dakarun soja sun ce kada a yi bikin. Daga nan ne suka fara neman Bamba da sharri.”
“Muna cikin damuwa da wadanda ke kwance a asibiti, musamman masu raunuka masu tsanani. Ko da yake mun samu labarin cewa an kama jami’an kuma an mika su ga ‘yan sanda, amma muna kira da a gudanar da bincike mai kyau da sulhu don zaman lafiya,” in ji shi.
KU BIYO MU A FACEBOOK