Sama da mutane dubu daya mazauna kauyen Tashar Biri suka tsere daga kauyen da ke Yatumaki a karamar hukumar Dan Musa a jihar Katsina yayin da ‘yan bindiga suka yi barazanar kai farmaki kauyen kan zargin kashe wani dan bindiga mai suna Gwaska da jami’an tsaro suka yi.
Daily Episode ta tattaro cewa an kama Gwaska ne a wani tarko da jamian tsaro suka samasa yayin da yaje tadi wajen yarinyar da ya tilastawa akan sai ya aureta mai suna Sabira
Don haka ‘yan fashin suka bukaci mutanen kauyen ko dai su mika masu Sabira da mahaifiyarta ko kuma su biya Naira miliyan 30 a matsayin haraji, ko kuma su kawao masu farmaki mai muni a matsayin ramuwar gayya kan kisan gillar da aka yi wa Gwaska.
Sai dai kuma bayan sabira da mahaifiyarta sun tsere, ‘yan fashin sun yi garkuwa da kakar Sabira da danta Aliyu, wadanda har yanzu suke tsare, kwanaki bayan kashe Gwaska.
‘Yan ta’addan mazauna yankin Gadawa ne, a cewar wani mazaunin garin Anas Aliyu, wanda ya yi imanin cewa suna zaune ne a Katsale, wani sansani na ’yan bindigar da wani fitaccen shugaban ‘yan fashin mai suna Mai Lore ke jagoranta, wanda ya addabi kauyukan da ke kewayen Danmusa da kananan hukumomin da ke makwabtaka da su.
Dama cen sun sace mana dabbobi dakuma yin garkuwa da mutanen mu dukda ansakesu bayan munbiya kudin fansa anma halinda ake ciki yanzu babu wanda yake da tabbacin tsira daga harin da suke shirin kai wa. Saboda haka, mun bar kauyen zuwa ƙauyuka da ke kusa.
Duk da cewa wasu sun koma wasu garuruwa, wasu kuma sun yi balaguro zuwa wasu jihohi, kasancewar ba mu da sansanin ‘yan gudun hijira a fadin jihar Katsina.
Malam Aminu yakara dacewa, Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ina ’Yantumaki, kuma abin takaici ne a ce muku ba kowa a kauyukanmu. Har ma muna jin tsoron komawa mu kwashe kayanmu da amfanin gona,”
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan ne ‘yan bindiga suka kai munanan hare-hare a garin Guga, karamar hukumar Bakori, da kuma unguwar Magama da ke karamar hukumar Jibiya, inda ‘yan sanda da wani farar hula suka rasa rayukansu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Katsina bai amsa tambayar da manema labarai na Daily Episode suka yi ba dangane da kashe-kashen ‘yan bindigar.