Babban Shugaban Rundunar ‘yan Sanda ta ƙasa Usman Alƙali Baba, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar yan sanda da akai wa take da ‘Operation dawo da zaman lafiya dole’ a jihar Enugu dake kudancin Najeriya.
Sabuwar rundunar zata yi yaƙi ne a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan domin dawo da cikakken zaman lafiya a yankin.
An gudanar da taron ƙaddamar da rundunar a ranar Talata a Micheal Okpara Square dake birnin Enugu, babban birnin jihar ta Enugu.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron kaddamarwan akwai gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi. Wannan na zuwa ne kwana biyu kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari Hedkwatar hukumar zaɓe INEC a jihar Enugu, inda suka ƙona motoci da wasu kayayyaki ranar Lahadi.
Rahotonni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun ƙona motoci shida a harin da suka kai ofishin INEC ɗin na jihar Enugu. Hakanan kuma a watan Afrilu, yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda biyu a harin da suka kai ofishin Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani jihar Enugu.