An Gudunar Taron Da Taya Murna Ga Sabbin Shuwagabannin Jam’iyyar Na Yankin Karamar Hukumar Kankara.
Jaridar Rana24 ta ruwaito daya daga cikin Jigogin Jam’iyyar Apc a karamar hukumar Kankara Hon. Faruk Lawal Jobe wanda shine Kwamishinan ma’aikatar kula da Kasafin kudi da tsare tsaren habaka tattalin arzikin jihar Katsina ya yi taron taya murna ga sabbin shuwagabannin jam’iyyar Apc na karamar hukumar ta Kankara ne dake cikin jihar Katsina.
Taron da aka gudanar a ajiya Lahadi 16/01/2022 afafafiyar ginin karamar hukumar Kankara dake Kan hanyar Funtua da zummar sada zumunci da kuma taya murna ga sabbin shugabannin Jam’iyyar da aka zaba tun daga matakin mazabu zuwa matakin karamar hukuma a cikin shekarar 2021.
Hon. Faruk Jobe ya nuna farin cikin shi ga sabbin shuwagabannin jam’iyyar, gamida yimasu fatan alheri na Allah ya tayasu riko, da ikon yin adalci bisa nauyin shugabancin da, Allah ya dora masu.
Hakazalika Hon. Jobe ya tallafawa sabbin da tsaffin shuwagabannin, Kungiyoyin watsa labarun zamani na Social Media da Kungiyoyin Matasan Karamar Hukumar da zunzurutun kudi har naira miliyan uku domin su sha ruwa.
Jawabin daya daga cikin manyan bakin da suka samu halartar wannan taro Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina Alhaji Bala Abubakar Musawa ya nuna jin dadi tare da godema Kwamishinan akan kulawa da ya yi da shugabannin jam’iyyar.
Alhaji Bala Musawa ya kara dacewa” Shugabannin jam’iyyar dasu tashi tsaye da Addu’a, da niyyar Allah ya yaye mana wadannan bala’o’i na rashin tsaro da muke fama dasu.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Funtua Alhaji Ibrahim Danjuma Malumfashi ya bayyana Kwamishinan matsayin mutum na farko da ya kira irin wannan taro tun bayan zabensu da akayi cikin shekarar da ta gabata.
Anashi jawabin Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar Kankara Alhaji Mansir Isiya Jeri ya godema Kwamishinan tare da yin Addu’a, Allah ya maida kowa gidansa lafiya.
Maitaimakawa Gwamnan Jihar Katsina na musamman akan maido da martabar Jihar Katsina Alh. Sabo Musa ya Jagoranci Addu’a ta musamman ta neman zaman lafiya ga karamar hukumar Kankara da Jihar Katsina da Najeriya baki daya.
Kadan daga cikin manyan bakin dasuka samu halartar wannan taro sun hada da mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon. Kabir Shu’aibu Charanci wanda ya samu wakilcin Darakta mai kula da harkar siyasa, Daraktan kudi da mulki na karamar hukumar Kankara dactakwaran shi na Dutsinma Alhaji Aliyu Haruna Kankara, Hon. Hadi Bello Ajir da Mataimakin Sakataren Jam’iyyar Apc na Jihar Katsina Alh. Umar Tsoho Mustapha da sauransu.
Daga karshe Hon. Yar’tsamiya ne ya rufe taro da addu’a.