Daga ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato an bayyana kisan akalla Mutane sama da Hamsin yayin wani sabon harin ta’adancin da aka kaima ƙauyen Irigwe dake Jos.
Kimanin Mutane Hamsin da Ɗaya 51 ne aka ƙiyasta kashewa yayin wani harin tsakar dare da aka kai yankin Zikke hamlet, Kimakpa dake gundumar Kwall masarautar Irigwe Chiefdom, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato a daren ranar Lahadin da ta gabata 13/04/2025.
An bayyana ɓarnatar da rayuka da dukiyoyi da dama a wannan yankin, a wani ƙaulin kuma an bayyana kai wani harin a yankin Mangu duk a jihar ta Filato inda aka kashe rayuka da ɓarnatar da dukiyoyi.
Gwamnatin jihar tayi kiran da akai zuciya nesa bayan da gwamnan jihar ya jajantama Mutanen yankunan da lamarin ya rutsa dasu, sannan kuma ya bayyana cewa daga yanzu.
An haramta kiwo da dare a faɗin jihar, sannan an hana ɗauka ko lodin shanu daga ƙarfe Bakwai na yamma, kazalika an hana zurga zurgar mashin daga ƙarfe Bakwai na yamma zuwa ƙarfe Shidda na safiya.
Haka nan kuma gwamnan ya bada umarnin kulawa da duk wanda aka kawo da raunika a Asibitocin dake yankunan da lamarin ya faru ya kuma yi alkawalin kawo agajin gauka ga yankunan abun ya shafa, sannan kuma masu gari su ƙarfafi ƙungiyoyin yan banga domin kulawa da yankunan su.