Wasu al’ummar kauyuka a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce tare suke shan ruwa da dabbobin da suke kiyo.
Wannan na zuwa ne daidai ranar da ake bikin ruwan sha ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai kimanin mutum biliyan biyu da ke fama da matsalar ruwan sha a duniya.
Malam Sani Isa wani mazaunin kauyen Gurin Gawa ne da ke jihar Kano, ya ce shi da ‘yaransa biyar ba sa kyamar ruwan da dabbobinsu ke sha saboda suma shi suke sha kamar yadda BBC ta ruwaito

