Majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗa Buratai tare da wasu tsofaffin manyan hafsoshin tsaron kasar a matsayin jakadun kasar.
Majalisar ta amince da nadin nasu ne a zamanta na ranar Talata, bayan nazari kan bukatar hakan da shugaban kasar ya tura busu a baya.
A ranar biyar ga watan Fabrairu ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da sunayen tsofaffin shugabannin tsaro na ƙasar ga Majalisar Dattawa don amincewa da su a matsayin jakadu na musamman.
Cikijn wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, ya fitar ta ce Buhari ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan wasiƙa, inda yake neman amincewarsu.
“Bisa tanadin sashe na 171 (1) da (2) (c) da sakin layi na (4) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima, ina mai neman amincewar Majalisar Dattawa don naɗa sunayen mutanen (5) da na lissafa a matsayin jakadu na musamman,” in ji Buhari.
Waɗanda za a naɗa sun haɗa da: Janar Abayomi G. Olonisakin (mai ritaya) da Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) da Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar ya nemi majalisar da ta gaggauta tabbatar da sojojin a kan matsayin nasu.
Mohammed S. Usman, shi kaɗai ne ba ya cikin manyan hafsoshin tsaron da Buhari ya sauke ranar Talata da ta wuce sannan ya maye gurbinsu da wasu domin ci gaba da jagorantar ayyukan tabbatar da tsaro a Najeriya.
Sabbin hafsoshin tsaron da aka naɗa su ne:
- Janar Leo Irabor – Babban Hafsan Tsaro
- Air-Vice Marshal I.O Amao – Babban Hafsan Sojan Sama.
- Rear Admiral A.Z Gambo – Babban Hafsan Sojan Ruwa
- Janar I. Attahiru – Babban Hafsan Sojan Ƙasa.
Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da zargin da ake yi na cewa ta ba su muƙaman ne domin kaucewa gurfanarsu gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, domin kare kai bisa tuhumar cin zarafin dan adam da aka yi karkashin jagorancinsu.