A duk lokacin da mtum ya rasu, ‘kabarinsa shine makwancin sa anma yanayinda makabartar hayin biliya dake rigasa karamar hukumar igabi jihar kaduna ke ciki abun ba dadi.
Domin ruwa na tona asirin wasu kabarurukan har yakan tafi dawasu sasa na gawawaki.
Yayin da zaizayar ‘kasa take cinye yawa yawan kabarorin saboda rashin hanyar ruwa da kuma kyakykyawan tsarin kabarurrukan, makabartar ta zama hanyar ruwa da kwatocin gidajen mutane wanda sanadiyydr hakan ya janyo budewar kabarurrukan da dama.
Me kula damaqabartar ya shaidawa wakilin Daily Episode cewa ko sun kira mutane don aikin gayya na gyaran maqabarta basa zuwa.
Sanan ya koka dacewa mutane basa zuwa damanyan itatuwa kuma hakan na janyo ruftawan kabaruruka dadama.
Kuma itama gwamnati bata daukar matakin da yadace wajen kulada makabartoci dukda akan samu wasu gurbatatun mutane masu satar sassan matatu.
Masu kula da makabartar sunayin aikine na sakai anma dukda haka suna bukatar kulawa ta musanman dakuma albashi Idan mukayi laakari da barazanar da rayiwarsu keciki dakuma aikin dasukeyi na kulada makabartar.
Saidai Malam Abdullahi ya shaidamana cewa babu wani tallafi dasuke samu daka wajen aluma ko gwamnati.
Duba da chanjin yanayi irin na damina a yayin gina kabaruruka akwai bukatar a samar masu da makari na kankare ko ginin bulo saboda gudun kar ruwa ya wanke kabarurukan.
Makabartar naneman tallafin gaggawa domin shawo kan matsalar da ta ke fuskanta.
Anyi kira ga gwamanati damasu hanu da shuni daama aluma dasu taimaka.